JABIRU A HASSAN, Daga Kano.
AN bayyana cewa mawakan siyasa sune gishirin dimokuradiyya idan aka dubi irin gagarumar gudummawar da suke baiwa harkokin siyasa tare da kasancewa masu aika sakonni na gyara kayanka ga al\’umar da ake yiwa shugabanci ko kuma shugabanni.
Wannan tsokaci ya fito ne daga fitaccen mawakin siyasar nan dàke jihar kano, Malam Sulaiman Leri Dawakin Tofa wanda akafi sani dà Sule nà Maroko a wata hirà da sukà yi da wakilin mu, inda ya ssnar da cewa ko shakka babu, mawakan siyasa sune suke fadakar da al\’ uma irin muhimman abubuwan dà kasa ke ciki ko kuma sahihancin mutanen da suke neman a zabe su kan mukamai dabàn-dabàn.
Haka kuma Malam Suleimàn na Maroko yace a tsari irin na dimokuradiyya, mawakan siyasa sune suke nuna amfànin mutane dake bukatar tàkara a jàm\’iyyu daban-daban ta yadda kowa zai duba nagartar wanda yàke so yà shugaban ce shi, tare da yin kira gà yàn uwansa mawakan siyasa da su rika mutunta mutanen da suke wasawa ko abokàn hamayyàr su domin ganin ana yin adawa mài amfàni.
Mawakin siyasar ya yi amfàni da wannan dama wajen yin fatàn alheri ga dukkanin mawakan siyasar dake kasarnan bisa yadda aka hadu ana aikin bunkasa dimokuradiyya, sannan yayi godiyà ta musamman ga iyayen gidàn sa na siyasa da masu neman madafar iko a matàkai dàbàn-daban dàke fadin kasarnan.
Daga karshe, Malam Sulaiman Leri na Maroko ya sanar dà cewa zai fitar dà wasu sabbin wakoki kan siyasar Nijeriya dà shirin zabukan 2019 da yaddà al\’uma zasu fàhimci alkiblàr ciyàr dà kasa gàba, inda kuma ya nunar da cewa dukkanin masu bukatar samun wakokin sa ko wani karin bayani sai a tuntube shi akan lambar sa ta waya 08065307878