Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
MAI kula da tafiyar da dukkan al\’amuran ofishin Jakadancin kasar Amurka da ke Nijeriya Mista David Young, ya bayyana wa manema labarai cewa sun Gamsu da irin yadda al\’ummar Jihar Osun suka gudanar da zaben Gwamna a Jihar.
David Young Wanda shi ne ke kula da tafiyar da dukkan al\’amuran ofishin Jakadancin Amurka a Nijeriya ya ce hakika irin yadda jama\’ar da suka yi zabe a Osun abin farin ciki ne da yakamata a yaba saboda an gudanar da Dimokuradiyya kamar yadda take a lokacin zaben na Osun.
\”Muna fatar za su ci gaba da yin zabe a Gobe Alhamis domin kammala zaben da ya rage cikin kwanciyar hankali da lumana kamar yadda suka aiwatar domin ci gaban kasa da kare tsarin Dimokuradiyya .
Da yake amsa tambayoyin manema labarai a kan tambayar irin yadda Nijeriya ke samun yawan karuwar Jama\’a kuwa, ya bayyana cewa ya dace a tashi tsaye wajen koyawa jama\’a sana\’o\’in hannu ta yadda za a samu bunkasar tattalin arziki, Ilimi da harkar lafiya.