Daga Usman Nasidi
JAM\’IYYAR PDP ta sanar da cewa za ta gudanar da zaben fidda gwani a jihar kaduna a ranar 30 ga watan Satumban shekarar 2018.
Jadawalin gudanar da zaben fitar da gwanin ya fito ne daga hannun Sakataren yadda labarai na jam\’iyyar, Abraham Alberah Katoh a wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.
Sanarwan ta ce jam\’iyyar ta PDP za ta gudanar da zabukkan fidda gwani a jihar Kaduna kamar haka: 1. Gwamnoni – Ranar 30 ga watan Satumban 2018 2. Sanatoci – Ranar 2 ga watan Oktoba 2018.
- \’Yan majalisar tarayya – Ranar 3 ga watan Oktoba 2018
- \’Yan majalisar jiha – Ranar 4 ga watan Oktoba 2018
- Babban taron jam\’iyyar PDP na kasa – Ranakun 6 da 7 ga watan Oktoban 2018.