Mustapha Imrana Abdullahi Daga Kaduna
YAN takarar Gwamnan Jihar Kaduna karkashin jam\’iyyar PDP sun fito fili inda suka bayyana korafin su a kokarin da suka bayyana cewa ana yi masu son zuciya.
Su dai Yan takara biyar daga cikin Yan takara sama da Goma duk sun fito fili sun shaidawa manema labarai cewa suna zargin shugaban jam\’\’iyyar PDP reshen Jihar Kaduna wato Mista Felix Hassan Hyat da zargin gayawa wani Dan takara baya a cikin su
Sun dai bayyana cewa yin hakan ya sabawa tsarin mulkin jam\’iyyar Babu inda wani ko wasu shugabannin PDP a Kowane irin mataki na neman wata kujera suke da ikon nuna wariya su goyi bayan wani
Sun dai bayyana hakan ne a wajen wani taron manema labarai da suka yi a cibiyar Yan jaridu a kaduna
Inda Yan takarar gwamna su biyar suka hade wuri guda domin kalubalantar Dan takarar da shugaban jam’iyyar yake marawa baya, Wanda hakan ya sanya suka ware gefe guda suka kafa wata kungiya Mai suna “Kaduna State PDP Aspirant Unity Forum ” da zimmar Fitar da mutum daya daga cikin su domin kalubalantar Wanda suka bayyana da cewa dan takarar shugaban jam’iyyar ne wato Mohammed Isah Ashuru.
‘Yan takarar, sun kuma zargi tsohon gwamnan jihar, kuma tsohon shugaban jam’iyyar PDP Na kasa, Sanata Ahmed Makarfi, Da shirya makarkashiya Wajen goyon bayan wani Dan takarar.
Sai dai a wata sanarwa, Sanata Makarfi, ya karyata zargin inda yace shi bashi da Dan takara.
‘Yan takarar Wanda suka hada da Suleiman Hunkuyi da Muhammad Sani Sidi da Mukhtar Ramalan Yero da Muhammad Sani Bella da Kuma Shu’aibu Idris Mikati.
A wani taron manema labarai da suka Kira, sun bayyana cewa shugaban jam’iyyar PDP Na jihar Felix Hassan Hyet, yana goyon bayan Mohammed Isah Ashuru, Wanda yana daga cikin ‘yan takarar gwamna, a cewarsu, Sanata Makarfi yayiwa shugaban jam’iyyar PDP albishir cewa idan Isah Ashuru ya lashe zaben fidda gwani Na jam’iyyar shi za’a bawa kujerar gwamnan jihar Wanda hakan ya sanya yake mara masa baya.
Shi dai Isa Muhammad Ashiru ya koma PDP ne sakamakon irin matsalar da ya samu na rashin Jituwa a jam\’iyyar APC da ya yi takara a karkashin ta a zaben shekarar dubu 2015.
Za dai ayi zaben fitar da Gwani a PDP a ranar 28 ga watan Satumba 2018 Ya zuwa Yanzu dai wannan rikicin jam’iyyar PDP yana iya haifar mata da cikas a zaben 2019, musamman ganin cewa rikicin yana neman ya sanya jam’iyyar ta dare gida.
Masu fashin bakin siyasa a jihar kaduna, tuni dama sukayi hasashen cewa jam’iyyar PDP Na iya fadawa cikin yakin basasar siyasa, musamman ganin kowanne Dan takarar gwamna yana da me gida Wanda sulhu a tsakanin ‘yan takarar zaiyi wahala matuka.
Abin Jira a Gani shi ne irin yadda PDP za ta warware wannan matsala da ta kunno Kai a cikin jam\’iyyar, ganin cewa suna kokarin kwato mulkin Jihar ne daga hannun Nasiru Ahmad El- Rufa\’i na APC