Rabo Haladu Daga Kaduna
TSOHON Gwamnan Jihar Jigawa da Sanata Shehu Sani na Jihar Kaduna sun tsallake Rijiya Da Baya, Yayin Da Man Jirgi Ya Kare musu, Suna Sararin Samaniyya.
Hankalin Fasinjoji Kimanin 60 Ciki Hadda Tsohon Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido Da Sanata Shehu Sani Na Jihar Kaduna Ya Tashi a Cikin Jirgin Saman Azman Da ya Nufi Abuja Daga Kano A Jiya Litinin, Yayin da Mai Ya Kare A Cikin Jirgin Kuma Suka Kasa Sauka Har Na Tsawon sa’o’i.
Kamar Yadda Wani Wanda Yake Cikin Jirgin Ya Bayyanawa Manema labarai Cewa Jirgin Mai Lamba ZQ 2332 Ya Tashi Daga Kano Da Misalin karfe 1:20 Na Rana Kuma Wanda Ya Kamata Ya Sauka A Abuja Da Misalin Karfe 2:05 Na Rana, Wanda Hakan Baiyuwuba.
Yace Direban Jirgin Ya Tuntubi Filin Jirgin Saman Domin Sauka Amma Suka Fada Masa Kada Ya Sauka Saboda Rashin Wajen Saukar Jirgi.
Direban Haka Ya yi Ta Shawagi A Sama Har Man Jirgin Ya Kare, Wanda Haka Ta Tillasawa Matukin Jirgin Sauka Duk Da Rashin Kyakkyawan Yanayi Wurin Saukar Jirgin.