YAJIN AIKIN GAMA-GARI: MUNA DA MAI NA WATA GUDA NE KACAL – NNPC

0
544

Daga Usman Nasidi

MATATAR man fetur ta kasa tace kwanaki 37 ya rage PMS wanda aka fi sani da fetur ya kare karkaf a kasar.

Matatar ta bayyana haka ne a wata takarda da mai magana da yawun ta yasa hannu, Mista Ndu Ughamadu, a ranar laraba a garin Abuja.

Yace manajan daraktan matatar, Dakta Makanti Baru, ya roki masu ababen hawa da sauran masu amfani da fetur da kada su tsorata su dinga siyan man suna boyewa saboda yajin aikin da kungiyar kwadago ta kasa ta fara.

Ya bayyana cewa Gwamnatin tarayya tana iya kokarin ta gurin sulhuntawa da kungiyar kwadago.

Ughamadu ya kara da cewa man fetur wanda zai isa Najeriya na kwanaki 37 ya rage a kasar.

Ya tabbatar da cewa duk wasu rassan matatar dake kasar, da kuma wadanda matatar ta yarje ma wa gurin siyar da mai zasu cigaba da siyar da kayayyakin man fetur domin amfanar yan kasa.

Matatar ta kara da cewa zata cigaba da tabbatar da cewa yan Najeriya na samu ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here