CIKAKKEN SAKAMAKON ZABEN GWAMNAN OSUN TSAKANIN APC DA PDP

0
554

Daga Usman Nasidi

A RANAR Alhamis, 27 ga watan Satumba, ne mutanen jihar Osun suka komawa filin zabe domin kada kuri’unsu a zaben raba gardama na gwamnan jihar da aka yi zagayen farko ranar Asabar.

Yanzu haka Gboyega Oyetola, dan takarar jam’iyyar APC ne a gaba a zaben bayan lashe mafi rinjayen kuri’u a kananan hukumomin Ife ta kudu, Ife ta arewa da Osogbo.

Ana gudanar da zaben raba gardamar ne a mazabu 7 dake kananan hukumomin jihar Osun 4 da suka hada da Ife ta kudu, Ife ta arewa, Orolu da Osogbo. Ga jerin sakamakon kamar yadda suke a mazabun da aka gudanar da zaben Orolu:

Mazaba ta 1: APC 150 PDP 005, Mazaba ta 2: APC 195 PDP 010, Mazaba ta 3: APC 160 PDP 010 Orolu, mazaba ta 8, akwatu ta 4 APC 198 PDP 15 Orolu, mazaba ta 9, akwatu 3 PDP 64 APC 41

Karamar hukumar Ife ta kudu, akwatu ta 012 APC 283 PDP 15 Ife ta kudu Mazaba ta 1. APC 355 PDP 005 Mazaba ta 2.(Garage Olode) APC 385 PDP 005

Mazaba ta 10, akwatu ta 02, karamar hukumar Ife ta arewa APC 126 PDP 2 Ife ta arewa (Oyere) APC 300 PDP 005 Mazaba ta 8, akwatu ta 10, karamar hukumar Ife ta kudu APC 172 PDP 21 Mazaba ta 5, akwatu ta 17,

karamar hukumar Osogbo APC 299 PDP 165 Mazabar Oyęrę Aborisade dake Ife APC=130 PDP=2 Mazabar Garage Olode Osogbo APC-485 PDP-5 Mazaba ta 08, akwatu ta 001, a Kajola APC 111 PDP 3

Yanzu haka APC ce a kan gaba da banbancin kuri’u fiye da 1,000 tsakaninta da jam’iyyar PDP. Har yanzu hukumar INEC bata bayyana wanda ya lashe zaben ba, wannan sakamako ne da aka tattara daga mazabun da aka maimaita zaben na raba gardama.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here