2019: DAGA KARSHE PDP TA SALLAMA WA DINO TIKITIN TAKARAR KUJERAN SANATA A KOGI

    0
    642

    Daga Usman Nasidi

    JAM’IYYAR Peoples Democratic Party (PDP) ta tabbatar da Sanata Dino Melaye a matsayin dan takarar tan a sanata a yankin Kogi ta yamma a zaben 2019.

    An gudanar da zaben fitar da dan takara ne a Prestige Hotel dake Kabba, hedkwatar yankin. Shugaban zaben, Mista Jude Sule yace Melaye ya lashe dukkanin kuri’un 800 harda na wakilai daga yankuna bakwai dake mazabar.

    Zaben wanda ya gudana cikin kwanciyar hankali ya samu kula daga hukumar zabe mai zaman kanta (INEC) da wasu jami’an tsaro.

    A halin da ake ciki, tabbatar da Dino Melaye ya zo da wasu lauje a cikin nadi domin kwamitin tantancewa na jam’iyyar sun ki tantance yan takara hudu yayinda wasu biyu suka janye masa hakan yasa ya zama bai da abokin adawa.

     

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here