A Yau Laraba Ake Gudanar Da Zaben Fidda Gwani A Zamfara

0
755

 

Rabo Haladu Daga Kaduna

A YAU laraba ne ake sa ran za a yi zaben fidda-gwani na masu neman takarar gwamna a karkashin jam`iyyar APC a Bihar Zamfara.

Sau uku ana sanya ranar zaben ana dagewa saboda wasu matsaloli. Amma dukkan bangarorin da ke rikici da juna a wajen wannan zaben sun sasanta da juna – kama daga bangaren gwamnatin Zamfara zuwa bangaren gungun wasu \’yan takara su takwas.

Shugaban kwamitin zaben fid da gwanin, Dakta Abubakar Fari ya kawar da duk wata shakka game da gudanar da zaben ranar Laraba:

\”Mun warware dukkan wasu matsaloli da ke son dabaibaye gudanar da zaben, daga safiyar Laraba za a yi zabe a dukkan matsabun jihar Zamfara.

An samu sabani tsakanin gwamnan Zamfara da mataimakinsa tun da farko dai gwamna Abdulaziz Yari na jihar ya kafe cewa ba za a guudanar da zaben fid da gwanin ba, domin wasu dalilai da suka hada da cin fuska da kuma rashin tuntubarsa da ya ce kwamitin shirya zaben bai yi ba.

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here