HADIMAN BUHARI BIYU SUN YI FADA A KAN ZABEN FITAR DA DAN TAKARAR GWAMNA A APC

    0
    550

    Daga Usman Nasidi

    AN samu afkuwar abin kunya ranar Lahadi tsakanin wasu manya a kasar nan kuma jigo a APC a kan zaben fitar da dan takarar gwamna a jihar Akwa Ibom.

    Wannan abun kunya ya faru ne tsakanin Ita Enang, mai bawa shugaba Buhari shawara a kan harkokin da suka shafi majalisar dattijai, da kuma James John Udo-edehe, mutumin da Buhari ya nada a matsayin mamba a hukumar NITDA.

    An fara samun hargitsi ne bayan isowar kayan aikin gudanar da zaben fitar da dan takarar gwamna da aka sauke a filin tashi da saukar jirage na jihar Akwa Ibom dake garin Uyo.

    Wata majiya ta bayyana cewar bayan an kai kayan zaben sakatariyar APC ne sai Enang, da hadin bakin Akpabio, ya isa ofishin jam\’iyyar domin dauke kayan.

    Kokarin dauke kayan zaben da Enang ya yi ne ya saka Udo-edehe ya mare shi tare da binsa da naushi. A kokarinsa na tsira daga bugun da yake sha ne, Enang ya ciji Udo-edehe a hannun domin ya samu kubuta.

    Duk da ya yi nasarar kubucewa, da kyar jami\’an tsaro suka yi nasarar ceton shi saboda kafin ta fito daga ofishin jam\’iyyar tuni yaran Udo-edehe sun sace tayoyin motar sa.

    Da yake magana da manema labarai bayan kammala zaben fitar da dan takara, Udo-edehe, ya nuna yatsan da Enang ya cije shi tare da bayyana shi a matsayin maci amana.

    Kokarin jin ta bakin Enang bai samu ba. Kazalika mai taimaka masa a bangaren yada labarai, Essien Inyang ya ki yin magana da manema labarai a kan lamarin.

    Wata majiya ta bayyana cewar sai da aka duba lafiyar Enang a wata cibiyar kula da lafiya.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here