UWAR JAM’IYYAR APC TA YI FATALI DA AMININ EL-RUFAI DAGA TAKARAR SANATA

0
1190
Adawa suke da junansu koko dai siyasa ce?

Daga Usman Nasidi

UWAR jam’iyyar APC ta watsa ma gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai kasa a idanu game da takarar kujerar Sanatan Kaduna ta tsakiya da yake muradin hadiminsa Uba Sani ya tsaya don ya fafata da Shehu Sani, sanata mai ci.

A ranar Talata 2 ga watan Oktoba ne aka shirya gudanar da zaben fitar da gwani na yan takarar Sanatocin jam’iyyar APC a jahar Kaduna, sai dai zaben bai yiwu ba sakamakon matsalar da aka samu game da jerin sunayen yan takarar da jam’iyyar APC da uwar jam’iyyar ta fitar.

Daga cikin fitattun yan takarkarun da jam’iyyar ta haramta ma tsaya takarar sanata a jihohin Najeriya akwai tsohon babban sufetan Yansandan Najeriya, Suleiman Abba daga jihar Jigawa, da Uba Sani, mashawarcin gwamna El-Rufai akan harkar siyasa.

Sai dai wannan matakin da uwar jam’iyyar ta dauka yayi ma Sanata Shehu Sani dadi sakamakon takun sakar dake tsakaninsa da gwamnan jahar, wanda ya sha alwashin sauko da Shehu daga mukamin da yake kai.

Amma rahotanni sun tabbatar da cewar a yanzu haka an dage gudanar da zaben na fidda gwanin yan takarkarun Sanatocin na jahar Kaduna sakamakon hatsaniyar da ta taso a dalilin wadannan sunaye da jam’iyyar ta fitar.

Amma duk da haka wannan matakin da APC ta dauka bai hana magoya bayan Sanata Shehu Sani bayyana farin cikinsu ba, musamman yadda suke ganin alamu sun nuna sune masu nasara tunda dai an yi watsi da Uba Sani, wanda hakan ke nufin zai fito takara babu hamayya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here