AKAN SHEHU SANI:  EL-RUFA’I YANA GANAWAR GAGGAWA DA SHUGABA BUHARI

0
687

Daga Usman Nasidi

LABARIN da ke shigowa da duminsa na nuna cewa gwamnan jihar Kaduna, Naisr Ahmed El-Rufa’I da gwamnan jihar Ondo Rotimi Akeredolu, sun shiga ganawar sirri da shugaba Muhammadu Buhari a fadar shugaban kasa ta Aso Rock, Abuja.

Gwamnonin biyu sun isa fadar shugaban kasan ne misalin karfe 3:15 na ranan nan. Har yanzu suna cikin ganawar yayinda muke kawo muku wannan rahoto.

Za ku tuna cewa gwamnan jihar Kadunan na cigaba da hamayya da Sanata Shehu Sani tun kimanin shekaru uku yanzu.

A yayinda zabe ya gabato, sanatan ya nemi ayi sulhu amma gwamnan yace ba zai yard aba sai ya sauyashi.

Hakan ya sanya Sanatan ya nemi agajin jam’iyyar APC ta kasa domin sulhuntasu. Mataki na farko na yin sulhu shine cire takunkunmin da jam’iyyar ta sanya masa a matsayin dan jam’iyya, amma bangaren jam’iyyar ta jiha ta nuna rashin amincewarsa da wannan afuwa.

Daga karshe yayinda ake shirin gudanar da zaben fidda gwanin kujerar sanata maso tsakiya na jihar, jam’iyyar ta kasa ta baiwa Sanata Shehu Sani goyon bayan yayi takara shi kadai yayinda taki tantance wanda gwamna El Rufa’I, wanna abu ya jawo tashin hankali da zanga-zanga a jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here