Mustapha Imrana Abdullahi
KAKKARFAN kwamitin da uwar Jam\’iyyar APC ta kasa ta aika Jihar zamfara domin gudanar da zaben fitar da Gwani a tsakanin Yan takarar da ke Neman kujerar Abdul\’aziz Yari Abubakar kwamitin ya bayyana soke zaben da aka yi a wadansu wurare.
Wannan sanarwa ta biyo bayan irin yadda aka samu tashe tashin hankali ne a wasu kananan hukumomi Wanda sakamakon hakan ba a samu gudanar da zaben ba.
Rahotanni sun tabbatar da cewa ko a cikin garin Gusau da kuma sassan karamar hukumar akwai inda aka samu matsalar rashin Kai kayan aiki a kan lokaci Wanda wannan ma dalili ne babba da ya hana a gudanar da zaben.
A wadansu wuraren an dai samu matsalar kone kone Tayoyi kamar a Bungudu da lamarin ya zamanto sai da aka yi amfani da Barkonon tsohuwa kafin a Tarwatsa masu tarzoma.
Akwai dai zargin da ake yadawa cewa an samu wasu jami\’an Gwamnatin Zamfara da Laifi a gudanar da zaben.