Zaben Cikin Gida: An Yi Takara Tsakanin Uwa Da \’Da A Jam\’iyyar APC

  0
  635

  Daga Usman Nasidi

  HAJIYA Khadija Ibrahim, karamar ministar harkokin kasashen waje, ta kayar da Mohammed Ibrahim, dan mijinta, Bukar Abba Ibrahim, a zaben fidda \’yan takara na APC a jihar Yobe.

  Khadija da Mohammed sun yi takarar neman kujerar majalisar wakilai ta kasa mai wakiltar Damaturu/Gulani/Gujba/Tarmuwa a jihar Yobe. Da yake sanar da sakamakon zaben, Farfesa Abba Gambo, ya ce Khadija ta samu kuri\’u 1,295 yayin da Mohammed ya samu kuri\’u 15 kacal.

  Rahotanni sun bayyana cewar duk kokarin shawo kan Mohammed domin ya janyewa Khadija, matar mahaifinsa, bai yi nasara ba.

  Ta kara da cewa ragowar \’yan takarar kujerar biyu da suka hada da Abdullahi Kukuwa, dan majalisar dake kai yanzu, da Alhaji Ahmed Buba sun janyewa Khadija takarar da suka fito.

  Sanata Bukar Abba Ibrahim bai halarci ko daya daga cikin zabukan fitar da \’yan takara da aka yi a jihar Yobe ba, har wanda matarsa da dan sa suka fafata.

  Sai dai wasu daga cikin daliget da suka halarci zaben sun yi alla-wadai da gazawar \’yan takarar na sulhunta kan su a cikin gida tare da bayyana cewar hakan ya nuna cewar akwai matsala a cikin gidan Bukar Abba.

  LEAVE A REPLY

  Please enter your comment!
  Please enter your name here