An Sake Gabatar Da Shaida A Kan Sule Lamido Na Batar Da Naira Biliyan 1.3

0
400
Rabo Haladu Daga Kaduna
SHAIDAR masu shigar da karar, wanda kuma jami’in hukumar ta EFCC ne, Michael Wetkas, ya sake bayar da karin bayanai a kan yadda ake zargin tsohon gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido, ya karkatar da wasu kudade da aka ware domin gudanar da ayyuka don amfanin kansa ta hanyar kamfanin Dantata and Sawoe.
A yayin da aka koma sauraron karar a ranar 20 ga watan Fabrairun 2020, binciken EFCC ya nuna yadda aka tura wa kamfanonin Sule Lamido Speeds International Limited da Bamaina Holding Company, makudan kudade a asusunsu na banki ta hanyar cakin kudin kamfanin Dantata and Sawoe a shekarun 2007 da 2013.
Kazalika akwai wasu kudade da aka biya ta hanyar cakin kudin da ya kai N7,408,000 da 7,425,000 daga asusun bankin Zenith na kamfanin Dantata and Sawoe da aka sunan Bamaina Holding Company.
Haka kuma shaidar ya bayyana cewa a ranar 23 ga watan Afrilun 2013, akwai wasu cakin kudi biyu da suka kai N7,228,900 daga asusun bankin Zenith da aka biya kamfanin Speeds International Limited.
Haka an biya kamfanin Speeds International Limited kudi N9,450,000 a ranar 19 ga watan Oktoban 2010, da kuma sauran kudaden da aka biya daga bankin UBA.
Shaidan ya gabatar da cakin biyan kudin a matsayin hujja.
Mai shari’a Ojukwu, ya dage sauraron karar har zuwa ranar 27 da 28 da 29 da 30 ga watan Afrilu da kuma 4 da 5 da 6 da kuma 7 ga watan Mayun 2020.
Idan za a iya tunawa, hukumar ta EFCC ta kara gabatar da tsohon gwamnan Sule Lamido da ‘ya’yansa biyu da kuma sauran jama’a a gabatn kotu bisa zargin cuwa-cuwar sama da N1.3

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here