Cika Shekara 60 Na Gwamna EL-Rufai Ya Amfani Al”ummar Nijeriya -Munkailu

0
497

 

Rabo Haladu Daga Kaduna

SHUGABANNIN Kungiyyar Kananan Hukumomi Takasa Reshen Jihar Kaduna (NLGE) sun bayyana cikar Shekara 60 da  gwamna Malam Nasiru  Ahmed EL_Rufai yayi cewa mai albarka kuma abar alfahari ga Al”ummar Jihar Kaduna dama Kasa bakidaya, Alhaji Munkailu Ibrahim Makarfi ne kuma daya daga cikin Shugabannin Kungiyar NLGE yabayyana haka ga  manema labarai a Kaduna.

Acewar Munkailu Cikar Malam Ahmed Nasiru EL_Rufai shekaru 60 da haihuwa wata babar nasarace ga kasarnan sabo da irin basirar da Allah yabashi na iya shugabanci da zaisa kowanne dankasa ya shaida haka idan akayi dube da zamansa ministan Abuja irin yadda ya gyarata tamkar Ingila,haka kuma Jihar Kaduna tunbayan da yazama gwamna yaketa aikace aikace nacanja mata fasali wanda inkashiga kaduna Kasan tahadu da katafila sarkin aiki .

Acewarsa raban da jihar kaduna tasami aiki irin wannan jajirtacen shugaba tun lokacin Sardauna.

Yace gwamna Malam Nasiru Ahmed EL_Rufai  yacancanci jinjinawa idan aka duba bangaran kiwan lafiya, ilimi, aikin gona, ruwansha, tàre da zama gwamnan farko da yafara biyan saban karin albashi nakashi 30 cikin 100.

Akarshe yayi kira ga jama”ar kasarnan dasu yi koyi hade da goyan baya ga gwamna Nasiru tareda cigaba dayiwa kasarnan addu”ar fatan samun zaman lafiya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here