Hukumar AMCON Ta Karbe Kamfanin Buba Galadima Saboda Bashin Miliyan 900

0
373
Mustapha Imrana Abdullahi
HUKUMAR kula da bankuna a tarayyar Nijeriya AMCON ta kwace gida da kamfanin Buba Galadima, wanda ya kasance a can baya makusancin shugaba Muhammadu Buhari ne na Nijeriya.
Kamar yadda rahotannin suka nuna cewa an karbe wadannan kadarorin ne saboda “wani bashin da ya kai miliyan dari Tara” (900).
Jami’in hulda da jama’ a na hukumar AMCON Jude Nwauzor, ya bayyana hakan a cikin wata takardar sanarwa a ranar Talata.
Ya ce Galadima da kamfaninsa na  Bedko Nigeria Limited suna rike da bashin AMCON da ya kai kusan miliyan dari 900 da aka karba daga Bankin Unity a shekarar 2011.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here