Manajan Kungiyar Kwallon Kafa Na Kano Pillars Ya Rasu

0
343

 Mustapha Imrana Abdullahi

BAYANAN da muke samu daga Jihar Kano na cewa manajan kungiyar kwallon kafa na Kano Pillars Kabiru Baleria ya rasu yana da shekaru 57 a duniya.

Mai magana da yawun kungiyar, Rilwanu Malikawa Garu ne ya tabbatar da hakan.

Ya dai rasu ne a Kano a wani asibiti mai suna (Doctors Clinic) bayan fama da wani rashin lafiyar da ba a bayyana ba.

Kuma tuni aka yi Jana’izarsa kamar yadda addinin Islama ya tanadar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here