Mustapha Imrana Abdullahi
DA dumi-duminsa: labarin da muke samu a yanzu na bayanin cewa shugaban majalisar dokokin Jihar Kaduna Alhaji Aminu Abdullahi Shagali ya sauka daga mukaminsa na shugaban majalisar.
Kamar yadda muka ga takardar ajiye aikin da ya rubuta da hannunsa ya kuma sanya mata hannu daga karshe kamar yadda ka’idar rubuta irin wannan takarda ta tanadar cewa ya ajiye aikin ne domin kashin kansa.