An Rantsar Da Sabon Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Kaduna

0
518

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

‘YAN majalisar dokokin jihar Kaduna sun zabi Honarabul Yusuf Ibrahim Zailani matsayin sabon kakakin majalisar a ranar Talata, 25 ga Febrairu, 2020.

An zabe shi ne kimanin awa daya bayan Honarabul Aminu Abdullahi Shagali ya yi murabus daga kujerar shugabancin majalisar.

Honarabul Yusuf Ibrahim Zailani wanda ke wakiltar mazabar Igabi ta yamma, ya kasance mataimakin kakain majalisar kafin aka zabe sa matsayin Kakaki a ranar Talata. Zailani babban jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ne a jihar Kaduna.

Hakazalika, an nada Honarabul Mukhtar Isa Hazo, mai wakiltar Bassawa matsayin sabon mataimakin kakakin majalisar jihar. Tuni Magatakardar majalisar ya rantsar da su.

Tsohon kakakin majalisar wanda ke wakiltar mazabar Sabon-Gari ya yi murabus ne a safiyar Talata.

Mun tattaro cewa mambobin majalisar sun fara rattaba hannun tsige sa ne kafin ya guji abin kunya ya yi murabus.

Amma har yanzu ba mu samu labarin abin da ya sa ake kokarin tsige sa ba.

Aminu Shagali ya zama kakakin majalisar dokokin jihar ne a shekarar 2015 da jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya lashe zabe a 2015.

Bayan karewar wa’adinsa na farko, an sake zabensa bisa ga alfarmar Gwamnan jihar Kaduna, Nasir Ahmed El-Rufa’i

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here