Bayan Shekaru 14 Da Rufe Ma’aikata, Ana Ci Gaba Da Biyan Ma’aikatan Albashi

0
551

Daga Usman Nasidi.

WANI kwamitin majalisar wakilai a ranar Litinin, ya gano cewa bayan shekaru 14 da aka yi da kulle Hukumar Hako Ma’adanai ta Najeriya, ma’aikatan na ci gaba da karbar albashi daga gwamnati.

Shugaban kwamitin, Oluwole Oke, ya umarci ministan ma’aikatar ma’adanai da karafa, Olamilekan Adegbite, Ministan ruwa, Suleiman Adamu da daraktan hukumar aiyukan gwamnati, Alexander Okoh da su gurfana gaban kwamitin.

Adegbite da Okoh zasu yi bayanin dalilin da yasa ma’aikatan cibiyar gwamnatin da aka rufe tun 2006 suka ci gaba da karba daga dukiyar gwamnati.

Mataimakin babban manajan sashin kudi na hukumar hako ma’adanan, Dauda Gambo, ya sanar da kwamitin cewa an rufe hukumar ne sakamakon komawa da za ta yi mai zaman kanta tare da hadin guiwar BPE.

Hakazalika, kwamitin ya gano cewa kusan tsoffin ma’aikatan kasuwar duniya ta Legas 24 wadanda aka kora suke ci gaba da karbar albashi daga hukumar.

Kwamitin ya mika takardar tuhuma ga RBDA don jin dalilin da ya hana su mika yadda suka kashe kudinsu ba, ga ofishin babban oditan tarayya.

Kwamitin ya kara da barazanar bada umarnin damko duk wani shugaban ma’aikata, bangare ko cibiya karkashin gwamnatin tarayya, wacce ta
kasa bayyana gabanta don kare yadda ta kashe kudinta.
Oke ya sanar da wannan ne a wani bayani da yayi a Abuja a ranar Litinin a kan zargin wasu cibiyoyi da boye-boye.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here