Daga Usman Nasidi.
MINISTAR walwala, jinkai da harkokin jin dadin al’umma, Sadiya Umar Faruq, ta bayyana dalilin da ya sa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi afuwa ga wasu daga cikin ‘yan Boko Haram masu tayar da kayar baya.
Bisa ga bayaninta, an yafe musu ne saboda ana bukatar su yi tunani su bar ta’adanci ta yadda za’a ba su taimako a wurare daban-daban na ci gaban rayuwa.
Sadiya Umar Faruq ta bayyana haka ne lokacin ta karbi bakuncin wakilan shugaban hafsoshin tsaro, Janar Abayomi Gabriel Olonishaki, karkashin jagorancin kwamandan rundunar atisayi Operaton Safe Corridor, Janar Bamidele Shaffa a Abuja.
A jawabin da mataimakin darektan sadarwar ma’aikatar, Rhoda Ishaku Iliya, ya rattafa hannu, Minista Sadiya ta ce: ” A cikin kokarin da gwamnatin Buhari take na cimma burinta a wurin kawar da rashin tsaro da masu tayar da kayar baya, gwamnatin tarayya ta kaddamar sa shirin afuwa ga ‘yan Boko Haram da suka tuba domin sauya tunaninsu ta yadda za a ba su taimako a wurare daban-daban na ci gaban dan Adam.”
Ta yaba wa jajircewa da kokarin rundunar wajen kokarin kawar da kalubalen rashin tsaro da wadannan masu tayar da kayar baya da kuma dawo da su cikin hayyacin su.
Ta kara da cewa wannan al’amari yana da matukar mahimmanci musamman a Arewa maso gabas a yau.
A nasa bangaren, Shaffa ya ce: ”Dukkansu suna lafiya a garuruwansu kuma babu wani karar rashin jituwa a kansu ko kuma wani korafi da aka kawo a kansu.”
Ya kara da cewa ba wani shirin shigar da su aikin soja kamar yadda wasu suke yadawa.