Rabo Haladu Daga Kaduna
DA alama mabarata sun bijire wa matakin da gwamnatin jihar Kano ta dauka na haramta bara a titunan jihar.
Ranar Talata ne Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce gwamnati ta dauki matakin ne domin tabbatar da tsarinta na ba da ilimi kyauta kuma dole ga ‘yan firamare da Sakandare a fadin jihar.
Sai dai kwana guda bayan gwamanti ta haramta bara, wakilinmu ya zaga birnin na Kano inda ya ga mabarata na ci gaba da gudanar da barace-barace, kan titinan jihar Kano.
Ya ce daga yanzu dole ne makarantun allo su shigar da darussan turanci da lissafi cikin tsarin koyarwarsu.
Gwamnan ya ce “idan har kana zaton cewa ba za ka karbi tsarin nan na mu ba, to sai dai ka bar jihar.”
A yayin jawabin, Ganduje ya bayyana cewa daga yanzu duk yaron da aka kama yana bara to za a kamo mahaifinsa ko mai kula da shi, kuma a gurfanar da shi gaban kotu saboda rashin mutunta dokokin
jihar.
Ko a makon jiya ma sai da Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi II ya yi kira ga gwamnatoci da su ringa kama duk wani mahaifi da aka samu dansa yana bara da sunan karatun Alkur’ani.
Matsalar bara musamman ga yara kanana na daga abinda ake dauka a matsayin daya daga cikin manyan matsalolin dake addabar arewacin Najeriya.
Wasu alkaluma na nuna cewa akwai fiye da yara Miliyan uku da ba sa zuwa makaranta, kuma mafi yawansu suna yankin arewacin kasar ne.
A baya ma gwamnatoci a jihar ta Kano sun taba hana bara, sai dai matakin bai yi tasiri ba, saboda abinda wasu masana ke cewa rashin ingataccen tsari da tanadi.