An Dakatar Da Sallar Juma’a Da Khamsu-Salawati A Kasar Iran

0
612

An Dakatar Da Duk Wani Sallar Juma’a Da Khamsu-Salawati A Kasar Iran

Daga Usman Nasidi.

MA’AIKATAR kiwon lafiyar kasar Iran ta yi sanarwa ranar Alhamis cewa an dauki wasu sabbin matakan dakile yaduwar cutar Coronavirus da ta addabi kasar cikin makon nan.

Daya daga cikin matakan shine dakatar da Sallar Juma’a har ila ma sha’a llahu.

Ma’aikatar ta bayyana cewa an haramta duk wani taron baja koli, khamsu-salawati, gidajen Sinima, bukukuwa, jana’iza, i’itikafi da duk wani gangami a kasar.

Shugaban sashen yada labaran ma’aikatar, Kianush Jahanpur, ya ce an kara yawan cibiyoyin gwajin cutar Coronavirus daga biyu zuwa bakwai, kuma za’a kara zuwa 15 kafin karshen makon nan, kuma 22 a makon gobe.

Hukumomin kasar Iran sun sanar a ranar Laraba cewa adadin wadanda suka rasa rayukansu sakamakon cutar ya tashi zuwa 19 kuma mutane 139 suka kamu.

Bugu da kari, kasar Iran ta kulle dukkan makarantu, jami’o’i, cibiyoyin Ilimi a garin Qom da Arak.

Rahotanni sun bayyana cewa Mataimakiyar shugabar kasar Iran kan harkakokin mata da Iyali, Masoumeh Ebtekar, ta kamu da cutar Coronavirus da ta addabi duniya.

Masoumeh Ebtekar ce mambar majalisar zartarwar kasa ta farko da zai kamu da cutar tun lokacin da ta bulla a Iran.

Shugaban kwamitin harkokin wajen Iran na majalisar dokokin kasar, Mojitaba Zolnour, ya bayyana a wani faifan bidiyo cewa shi ma ya kamu da cutar ta Coronavirus.

Hakazalika wani dan majalisa, Mahmoud Sadeghi da mataimakin ministan kiwon lafiyar kasar, Iraj Harichi, sun tabbata da kamuwa da muguwar cutar.

Bugu da kari, gidan talabijin kasar ta sanar a ranar Alhamis cewa babban Malami Hadi Khosroshahi, ya mutu sanadiyar kamuwa da cutar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here