EFCC Ta Sake Gurfanar Da Jang Gaban Kotu

0
407

Isah Ahmed Daga Jos

HUKUMAR da ke yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC ta sake gurfanar da tsohon gwamnan jihar Filato, Sanata Jonah David Jang  da tsohon  mai ajiya da bayar da kuxi, a ofishin sakataren gwamnatin jihar, Mista Yusuf Pam a gaban kotu kan zargin almundahanar kudaden Jihar Filato.

Hukumar ta gurfanar da su ne a  gaban Mai Shari’a C.L Dabup a kotun Jihar ta Filato, kan zarge-zarge 17.

Tun a baya dai, an taba kai wannan kara a gaban Mai Shari’a Longji, kafin ya yi ritaya daga alkalanci,  a ranar  31 ga watan Disambar bara, ya soke tuhumar da ake yiwa  wadanda ake zargin. Inda suke cewa ba su aikata laifin almundahanar ba, musamman kan maganar  kudaden kanana da matsakaitan masana’antu, da Babban Bankin Najeriya ya ba jihar, da kuma kudaden  hukumar ilmin makarantun firamare na bai daya [SUBEB] da ake zargin sun karkatar.

Daya daga cikin tuhumar da ake yiwa tsohon gwamnan an yi bayanin cewa a lokacin da yake kan kujerar gwamnan jihar, da tsohon ma’ajiyi da bayar da kudade a ofishin sakataren gwamnatin jihar, Mista Yusuf Pam. Daga watan Janairu zuwa watan Mayu na shekara ta 2015, sun yi almundahana da kudade N4,357,195,000 mallakar gwamnatin jihar, wanda hakan ya savawa kudin tsarin mulkin Najeriya, sashi na 309.

Wadanda ake zargin dai sun ki amincewa da laifukan da ake zarginsu da aikatawa. Lauyan da ke karar mutanen biyu, ya bukaci kotun ta saka ranar fara shari’ar.

Lauyoyin da ke kare wadanda ake karar E.G Phajok, (SAN), da S.G Ode sun bukaci a bayar da belin wadanda suke karewa, inda suka roki kotun ta tsaya kan belin da Alkali Longji ya bayar a can baya.

A karshe Mai Shari’a Dabup ta bayar da beli ga wadanda ake zargin, inda ta dora kan hujjojin Alkali Longji, kuma ta bukaci masu tsaya musu da su cika takardu, idan suna so su ci gaba da tsaya musu.

Mai shari’ar ta bayar da kwanaki uku, domin cika sharuddan belin, kuma ta sanya  ranar fara sauraron shari’ar  daga 26 zuwa 28 na watan  Mayu mai zuwa.


LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here