Gwamnati Ta Tallafa Wa Manoman Arewa Da Taraktocin Noma-Hassan Malami

    0
    539
    Alhaji Hassan Malami Barden Saminaka

    Isah Ahmed Daga  Jos

    Barden Saminaka Alhaji Hassan Malami, wani manomi ne kuma kwararre kan harkokin taraktocin noma da ya yi shekara da shekaru, yana gwagwarmaya kan wannan harka, ta taraktocin noma.

    Kuma shi ne shugaban kamfanin bayar da hayar taraktoci da sayar da kayayyakin gyaran taraktoci, na Ganyen Oda Investment Limited da ke garin Saminaka.

    A wannan tattauna da ya yi da wakilinmu, ya bayyana abin da ya karfafa masa gwiwar bude, wannan  kamfani a yankin  Saminaka.

    Har ‘ila ya yi bayanai da dama, kan harkokin taraktocin noma da harkokin noma gabaki daya. Ga yadda tattaunawar ta kasance:-

    GTK: Mene ne ya karfafa maka gwiwar bude wannan kamfani?

    Hassan Malami: Babban abin da ya karfafa mani gwiwar kafa wannan kamfani na bayar da hayar taraktocin noma da samar da kayayyakin taraktocin noma a wannan yanki na Saminaka. Shi ne ni dai na taso ne a gidanmu, naga ana yin noma, don haka tun ina karami na fara aikin noma.

    Bayan haka tun ina karami na kware kan harkokin taraktocin noma, don haka na san abubuwa da dama  kan harkokin taraktocin noma. Na ziyarci kamfanoni da dama da suke kera taraktocin noma a kasashe daban daban. Kuma nine ma’ajin kungiyar masu taraktoci ta Najeriya.

    Bayan haka babban abin da ya qarfafa mani gwiwar bude wannan kamfani a wannan yanki na Saminaka, shi ne mun kulla yarjejeniya ne da kamfanin qera taraktocin noma na Mahindara da ke Kasar Indiya.

    Za mu sanya masu adadin kudi na kashi 40, su kuma zasu sanya kashi 60, su  kawo mana sababbin taraktocin noma  da kayayyakin gyara na taraktocin noma, a wannan Karamar Hukuma ta Lere.

     Mun yi haka ne saboda muna ganin,  idan aka kawo taraktocin noma kuma aka kawo kayayyakin gyara,  za a sami gagarumar  nasara wajen bunkasa aikin noma, a wannan yanki.

    A wannan waje da muka bude  zamu rika bayar da hayar taraktoci muna zuwa muna  yiwa manoma manya da kananan aiki, a gonakinsu.  Duk wanda yake da bukatar mu yi masa aiki, za mu  je muka duba gonarsa mu auna ya biya mu yi masa aiki.

    GTK: Mene ne babban burinku kan kafa wannan kamfani?

    Hassan Malami: Babban burina game da wannan kamfani shi ne mu bunqasa harkokin noma, a wannan yanki. Domin idan muka kawo kayan aikin noman nan, muka yi amfani da su noman da muke yi a wannan yanki, zai nunka. Kuma muna da niyar muga mun bude rassan kamfani   a dukkan mazavun da suke wannan karamar hukuma  11.

    GTK: Mene ne banbancin aikin taraktocin noma  da aikin gargajiya da manoma suke yi da hanu?

    Hassan Malami: Gaskiya akwai banbanci kwarai da gaske, domin duk wajen da tarakto tayi aiki kuma aka sanya taki, amfanin gonar ba zaka haDa kyausa da  da irin amfanin gonar da manoma suka  noma da hanu ba. Idan a gona da manomi ya yi noma da hanu, zai sami buhu 10, idan ya yi amfani da tarakta zai iya samun buhu 15. Kuma  wurin da manoma 100 zasu yi aiki da hanu a rana, tarakto  zata iya yin wannan aiki a rana xaya.   Don haka muka bude wannan waje muka kawo taraktocin noma da kayayyakin gyara, domin mu taimakawa manoman wannan yanki.

    Duk wanda yake da wuri mai kyau, kuma tarakto tayi masa noma ba za ka hada shi da wurin da aka yi amfani da kayayyakin aikin noma, irin na gargajiya ba.

    GTK: Wadanne hanyoyi ne kake ganin gwamnati zata bi, ta samarwa  manoma taraktoci a kasar nan?

    Hassan Malami: A gaskiya hanyoyin da gwamnati zata bi ta samarwa manoma taraktoci a kasar nan suna da yawa. Amma  hanya ta farko ita ce gwamnati ta shiga maganar tallafawa manoma da taraktoci a kasar nan, musamman a yankin Arewa. A kalla gwamnati ta biyawa manoma kashi 30 bisa 100 na kudin tarakta a matsayin tallafi. Shi kuma manomi ya biya kashi 20 banki kuma su biya kashi 50. Idan aka yi haka za a sami nasara. Amma idan ya kasace babu  tallafin gwamnati a maganar taraktocin noma to akwai matsala. Saboda a yanzu babu manomin da zai iya cire maka kudi naira miliyan 13, ya sayi tarakto kwaya daya, sai dai babbban manomi. Don haka idan ana son a taimakawa kananan manoma, domin a karfafa masu gwiwa su koma gona, gwamnati ta shigo cikin wannan harka. Idan gwamnati ta shigo manoma manya da kanana za su amfana.

    GTK: Mene ne ra’ayinka dangane da bashin da ake baiwa manoma a kasar nan?

    Hassan Malami: Wato muna da manoma kashi uku a Najeriya. na farko akwai manoman da basa yin noman. Don haka idan aka basu bashin kayayyakin amfanin gona suna zuwa ne, su sayar.

    Bayan haka akwai manoma na gaskiya da idan aka basu irin wadannan kayayyaki suna tsayawa su yi aikin noman. Gaskiyar magana yawaicin irin wadannan manoma, suna sayar da kayayyakin ne suna cin abinci. Saboda wadansu ko an basu kayayyakin babu yadda za a yi, su iya yin noman.

    Sannan kuma na uku akwai manoman da su dama suna layin noman ne, idan aka basu kayayyakin zai taimaka masu.

    Amma gaskiyar magana mafi sauki shi ne gwamnati ta sake duba maganar bashin noman nan da take bayarwa. Gwamnati ta duba yanayin kowanne yanki da irin abubuwan da suke nomawa, wajen bayar da wannan bashi.

    Kuma ya kamata, gwamnati ta sake shigowa kan maganar taki, domin har yanzu manoma suna fama da matsalar rashin taki a kasar nan. Idan gwamnati ta shigo, manoma manya da kanana za su amfana.

    GTK: A karshe maye sakonka ga gwamnati kan harkokin noma a kasar nan?

    Hassan Malami: To sakona ga gwamnati shi ne ya kamata gwamnati ta kirkiro da  cibiyoyin hayar taraktocin  noma a yankunan karkara   na yankin arewacin qasar nan. Domin a riqa yiwa manoma aiki a gonakinsu kuma a sanya magunguna feshi  da taki a wadannan cibiyoyi a rika sayarwa manoma kan farashi mai rahusa.

    LEAVE A REPLY

    Please enter your comment!
    Please enter your name here