Daga Usman Nasidi.
HUKUMAR jin dadin alhazai NAHCON ta yi kira ga maniyyatan Hajjin bana da Umrah sun dakatar da duk wani shirye-shiryen ziyartar Makkah ko Madina har ila ma shaa’ llahu.
Kakakin hukumar NAHCON, Fatima Sanda, ta sanar da cewa an dakatar da shirye-shiryen Umrah zuwa kasar Saudiyya ne saboda matakin da kasa mai tsarkin ta dauka wajen kare kanta daga cutar Coronavirus.
Kawo yanzu, cutar ta yadu zuwa kasashe 48 kuma akalla mutane 82,164 sun kamu.
Mun kawo muku rahoton cewa Mahukunta a kasar Saudiyya sun hana maniyatta aikin hajji da Umrah shiga Makkah da Madinah domin gudun yada cutar Coronavirus da ke bazuwa a kasashen duniya.
Ma’aikatar harkokin kasashen waje ta Saudiyya ta ƙara da cewa za ta hana baki daga ƙasashen da aka tabbatar da bullar cutar ko inda ta ke barazana ga kiwon lafiyar mutane.
Har ila yau, ma’aikatar a shafin ta na Twitter ta kuma ce da dakatar da amfani da shedar katin ɗan kasa a madadin fasfo a lokacin shiga da fita kasar ta Saudiyya.