Rundunar Soji Ta Ceto Mutum 143, Wasu ‘Yan Boko Haram Sun Mika Wuya

0
467

Daga Usman Nasidi.

AKALLA mayakan Boko Haram takwas ne da suka hada da mata shida tare da kananan yara suka mika kai tare da yada makamansu. Sun mika kai ne ga runduna ta 152 da aka tura garin Banki da ke karamar hukumar Bama a jihar Borno.

‘Yan ta’addan, kamar yadda takardar da Kanal Aminu Iliyasu, shugaban yada labarai na rundunar ya fitar, ta ce ‘yan ta’addan da suka yada makaman sun hada da Tija Bo Isa, Ba Amodu Aba Kaka, Modu Zantalami, Malam Zantalami da Bakura Aba Kaka. Sauaran sun hada da Bulama Modu Zantalami, Abukar Izahi da Ban Katum.

“A yayin binciken farko, ‘yan ta’addan da suka yada makaman nasu sun nuna tsananin dana-saninsu na shiga cikin masu kashewa da garkuwa da mutane. Sun yi dana-sanin harar jami’an tsaro.” in ji takardar.

“Sun kara da bayyana cewa shugabancin kungiyar ta su ya kasance cikin halin rashin zaman lafiya tun watanni hudu da suka gabata yayin da aka fara kai musu farmaki. Hakan ya sa sun rasa manyan mayakansu,” ta kara da cewa.

“Sun kara da bayyana yadda abokansu suke yawo a daji kuma suna bukatar mika makamansu amma suna tsoron kada cibiyoyin tsaro su kashesu. A don haka suka yi kira ga abokan nasu da su jure tare da yin jarumtar fitowa su mika kansu ga rundunar sojin Najeriya din don hakan ne zai tabbatar da tsirarsu”, takardar ta ce.

Runduna ta biyar tare da hadin gwiwar batalliya ta biyu sun ceto da mutane 126 da mayakan Boko Haram din suka yi garkuwa da su. Sun samesu ne yayin da suke duba aiyukan rundunar sojin da ke karamar hukumar Guzamala ta jihar Borno. Wadanda aka ceto din sun hada da maza magidanta 36, mata 36 da kuma kananan yara 54.

A wani ci gaba makamancin hakan, runudunar soji ta musamman ta ceto da mutane 17 daga hannun mayakan Boko Haran din.

Kamar yadda takardar ta bayyana, duk wadanda aka tseratar din an mika su hannun jami’an sansanin ‘yan gudun hijira.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here