Daga Usman Nasidi.
WATA kotun Majistare a jahar Kaduna ta tsare wani Muhammad Isah kan zargin lalata da kananan yaransa mata su biyu.
Jastis Musa Lawal na kotun Majistare ya kuma dage sauraron shari’an zuwa ranar 30 ga watan Maris 2020, zuwa lokacin da zai zamana an gabatarwa da wanda ake zargin da sabbin tuhume-tuhume daga babbar kotun jahar.
Lauyan mai kara, Suleiman Ibrahim Kufena ya fada ma kotu cewa an gabatar da sabbin tuhume-tuhume a gaban babbar kotun.
Sai dai wanda ake kara, wanda lauyansa Murtala Baba Ibi bai halarci zaman kotu ba ya ce shi an sanar masa da batun amma bai sani ba ko an tura umurnin kotu zuwa ga lauyansa.
An tattaro cewa lamarin fyade ya yi karo na sashi na 258 na dokar jahar Kaduna ta 2017 kuma hukuncinsa na iya kasancewa daurin raid a rai yayinda a sashi na 370 na dokar kuma ya kan kasance akalla shekaru 14 a gidan yari.