Takaddamar Fili Tsakanin Jami’ar Jos Da Al’ummar Narakuta Ta Tayar Da Hankali A Jos  

0
543

Isah Ahmed Daga Jos

TAKADDAMAR mallakar fili tsakanin Jami’ar Jos da al’ummar Narakuta da ke makwabtaka da Jami’ar, ya kawo tashin hankali a garin Jos babban birnin Jihar Filato, da ya yi sanadin rasa ran wani mutum  mai suna Babangida Saudi Adam, tare da kona gidaje guda hudu da mota daya a ranar lahadin da ta gabata.

Shi dai wannan rikici ya taso ne a lokacin da ma’aikatan da hukumar Jami’ar Jos, ta turo suke aikin fitar da iyakar filin Jami’ar da garin na Narakuta, da ke makotaka da Jami’ar. Shi ne matasan garin suka fito, suka nuna rashin amincewarsu, a cikin wannan hali ne wani jami’in tsaro ya harbi, wannan mutum mai suna Babangida Saudi Adam, wanda rasa ransa.

Wannan abu da ya faru ya tayar da hankalin matasan wannan gari. Sai da jami’an tsaro suka yi iyakar kokarin su, kafin su shawo kan wannan al’amari.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Filato ASP Ubah Gabriel ya tabbatar da faruwar wannan rikici, kuma ya tabbatar da rasuwar mutum daya tare da kona gidaje guda 4  da mota 1 a wannan rikici. Amma ya ce tuni an shawo kan wannan rikici, jama’a sun ci gaba da harkokinsu na yau da kullum.

Wakilinmu ya gano cewar shi dai wannan fili da ake takaddamar malakarsa, tsakanin Jami’ar ta Jos da al’ummar na Naraguta da aka dauki lokaci ana yi, asalinsa na wani  kamfanin yin jan bulo ne,   mai suna Nigerian Bricks and Clay Products Limited da ke karkashin tsohon kamfanin hakar kuza na Najeriya.

A wata  sanarwar da ta fitar da ke dauke da sanya hanun mataimakin babban magatakardar Jami’ar ta Jos, Wilson Yale  ta bayyana cewa Jami’ar  ta sayi wannan fili ne daga kamfanin yin jan bulo na  Nigeria Bricks and Clay Product  LTD ta hanun kamfanin sayar da qadarorin gwamnati na BPE.

Sanarwar ta ce tun daga lokacin da Jami’ar ta mallaki wannan fili, wasu mutane suke ta shiga filin  suna gine gine.

‘’ A matsayinmu na masu bin doka da oda sai  muka kai wannan magana ga gwamnatin Jihar Filato. Wanda ya kai gwamnatin ta kafa wani kwamiti na mutum 10.  Don duba wannan al’amari, bayan da  kwamitin ya kammala aikinsa ya mika rahoto ga gwamnatin jihar. Ita kuma  ta fitar da farar takarda wadda ta tabbatar da cewa wannan fili, mallakar jami’ar Jos ne’’.

 A nata bangaren Kungiyar cigaban al’ummar Narkuta-Babale Bayan Doka tayi kira ga gwamnatin Jihar Filato da hukumar Jami’ar Jos, su tsaya su duba maganganun da suke kan wannan fili, kafin Jami’ar  ta cigaba da aikin fitar da iyakar filin. Kungiyar ta yi wannan kiran ne a wata sanarwa da ta rabawa ‘yan jarida   da ke  dauke da sanya hanun shugabanta, Alhaji Ibrahim Shu’aibu Muhammad.

Sanarwar tayi kukan cewa a matsayinsu na makotan   Jami’ar, Jami’ar  tayi watsi da su kuma ta  datse wa al’ummar garin  hanyar samun ruwan sha. Kuma    bata daukar yayansu suyi karatu a Jami’ar,  ko   basu aiki a Jami’ar.

Sanarwar ta yi kira ga gwamnatin Filato ta dubi mawuyacin halin da al’ummar Naraguta suke ciki, na rashin hanyar mota da ruwan sha, don ganin an warware masu wadannan matsaloli.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here