MAI bai wa shugaban karamar hukumar Dambatta shawara kan al'amuran mata Hajiya Alpha Abdu Usman Dambatta, wadda aka fi sani da" Maman Maja tace uwargidan gwamnan jihar Kano, Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje ta ciri tuta wajen samar da hanyoyi na bunkasa rayuwar mata da yara kanana.Tayi wannan bayani ne a wata ganawa da tayi da Gaskiya Taxi Kwabo, Ga kuma yadda hirar ta kasance: Daga Jabiru A Hassan. GTK: Hajiya a matsayin ki ta mace kuma yar siyasa wadda tayi fice wajen bayyana ra'ayinki kan tsarin dimokuradiyyar wannan kasa, me zaki ce dangane da sanya mata cikin gwamnati a jihar Kano?. Hajiya Alpha: To, da farko dai ina godiya ga Allah madaukakin sarki da ya bani damar kasancewa da wannan jarida wadda muke alfahari da ita. Sannan naji dadi da wannan tambaya domin inaso in sanar da cewa gwamnatin jihar Kano tayi rawar gani wajen baiwa mata mukamai masu yawan gaske wanda hakan ya nunar da cewa gwamnatin Dokta Abdullahi Umar Ganduje tana baiwa mata dama domin su bada tasu gudummawar wajen ciyar da jihar gaba a matakai daban-daban. Don haka gaskiya muna godiya ga wannan kokari da ake yi mana kuma zamu ci gaba da kasancewa masu kwazo da zummar taimakawa ci gaban jihar batare da nuna gajiyawa ba, fatan mu dai Allah ya kara mana nasarori da zaman lafiya a wannan kasa tamu mai albarka GTK: Matan gwamnoni suna bullo da ahirye-shirye domin kara kyautata rayuwar mata da kananan yara ta fannoni daban-daban, ko kuna samun irin wannan kokari a jihar Kano? Hajiya Alpha: Babu shakka mata a jihar Kano muna samun kulawa ta musamman tun a zangon gwamnatin Ganduje na farko, sannan yanzu abin yana karuwa duba da yadda mata suke da yawa cikin gwamnatin a wannan zango na biyu. Kowa yaga yadda uwargidan maigirma Gwamnan watau Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Ganduje take kokari wajen kawo shirye-shirye na iganta rayuwar mata da yara kuma Alhamdulillahi muna ganin tasirin ire-iren wadannan shirye-shirye a birni ya yankunan karkara. GTK: Kin yi bayanin cewa uwargidan Gwamna Ganduje tana bullo da ahirye-shirye na taimakawa mata da yara, kina ganin cewa nan gaba zaku zamo masu dogaro dakai kamar yadda ake fada? Hajiya Alpha: Inaso a game cewa a sanadiyyar kokarin da uwargidan Gwamnan Kano Farfesa Hafsat Ganduje take yi, mata masu tarin yawa suna cikin yanayi na rufin asiri saboda yadda aka basu horo kan sana'oi na dogaro da kai gashi kuma ana baiwa mata muhimmanci ta fuskar kula da lafiya da sauran abubuwa wadanda suke muhimmai kuma na yau da kullum. Babu lokacin da zai isa wajen bayyana gudummawar da uwargidan Gwamna Farfesa Hafsat Abdullahi Umar Gandujegaremu mu mata, sai dai in ce ta ciri tuta wajen kawo abubuwa na ci gaba garemu batare da nuna bambancin siyasa ko na ra'ayi ba. GTK: Mafiya lokuta mata suna korafin cewa ana barin su a baya duk da kokarin da kuke yi a yakin neman zabe da kafa gwamnatin, yaya abin yake a Kano? Hajiya Alpha: A matsayina ta daya daga cikin matan jihar kano, ina mai sanar da cewa matan jihar mu suna amfana da shirye-shiryen gwamnatin Ganduje ta kowane fanni. Sannan idan aka dubi mukamai da mata suke rike dasu kuma mukamai masu muhimmanci za'a yarda dani cewa matan jihar Kano ana tafiya dasu fiye da kowace jiha a kasarnan. Haka kuma dukkanin mukaman da maigirma Gwamna ya baiwa mata suna da tasiri wajen aiwatar da manufofin gwamnatin sa kuma babu wata matsala ta rashin amana ko kuma sakaci da aiki. Wannan lallai abin alfahari me garemu da uwargidan Gwamnan wadda a kullum take bamu horo da yin nasiha kan rike amana da taimakawa yan uwan mu mata wadanda suma suka sha gwagwarmayar neman zabe batare da nuna gajiyawa ba. GTK: Idan muka dawo kan batun siyasar Kano da yadda yan adawa suke kallon tafiyar gwamnatin Ku, ko akwai wani abu da kike ganin akwai matsala wajen tafiyar da jagorancin al'uma?. Hajiya Alpha: Kowa dai yaga yadda maigirma gwamna ya jagoranci jihar Kano a zango na farko, sannan yanzu ana ganin yadda yake tafiyar da gwamnatin a karo na biyu. Adawa a tsari irin na dimokuradiyya daidai ce amma ayi mai ma'ana wadda zata kawo sauyi da ci gaban al'uma. Zan iya cewa gwamna Abdullahi Umar Ganduje shine gwamna mafi kokarin daure adawa a Nijeria duba da yadda kowa ya ke fadar maganganu marasa tushe balle makama a Kansa kuma yake hadiyewa saboda yadda da yayi cewa jagoranci a dimokuradiyya yana haduwa da hamayya amma dai a rika fadar gaskiya. Wannan ce ta sanya yake cimma nasarori masu yawan gaske tareda kafa tarihi irin na siyasa a wannan kasa tamu, sannan shine gwamna mafi gudanar da aiyukan raya kasa da kawo sauyi a zamantakewar al'umar jihar sa duk da wannan adawa da yake sha tun a zango na farko lokacin ma bai shekara kan karagar mulki ba. GTK: Wadamne irin shawarwari zaki baiwa matan jihar Kano ganin yadda kuke amfanar wannan gwamnatin? Hajiya Alpha: A matsayina ta mai baiwa shugaban karamar hukuma shawara kan al'amuran mata, ina so yan uwana mata dake fadin wannan jiha da mu fahimci cewa Gwamnan Kano Ganduje yana kaunar al'umar sa gashi kuma uwargidansa ta kasance abar misali wajen bullo da shirye-shirye wadanda suke bunkasa rayuwar mu da kananan yara, don haka ina mai kira ga matan jihar Kano da mu kara godiya ga ubangiji saboda samun gwamnati mai kaunar mu. Sannan mu sani cewa uwargidan gwamna tana bukatar ganin muna cikin yanayi mai kyau don haka mu ci gaba da nuna mata godiyar mu da yi mata fatan alheri. GTK: Hajiya muna godiya da aka samu wannan dama muka tattauna abubuwa da suka shafi mata a wannan jiha. Hajiya Alpha: To nima nagode, kuma ina mai fatan alheri ga wannan jarida ta Gaskiya Tafi Kwabo wadda muke samun labarai da rahotanni sahihai kuma masu ilimantar wa duk Juma'a. Nagode kwarai.