Ba A Tantance Mutane Masu Shiga Najeriya A Filin Jirgin Sama – Sanata Boro

0
359

Daga Usman Nasidi.

MATAIMAKIN shugaban masu rinjaye a majalisar dattawa, Ajayi Boroffice ta bayyana cewa babu abin da ake yi domin kare Najeriya da annobar cutar Coronavirus.

Yayin da yake magana a zauren majalisar yau Alhamis, Sanata Boroffice ya ce yayin da ya dira babban filin jirgin saman kasa da kasa na Abuja daga kasar Afrika ta kudu ranar Laraba, bai ga ana duba masu shigowa kasar ba.

Ya ce ina ma ‘yar takarda ake bai wa mutane su rubuta ko suna da lafiya ko ba su da lafiya.

Ya kara da cewa a kasar Afrika ta kudu da ya je, sai da aka tantance su kafin sauka daga cikin jirgin.

Ya ce: “Ina kasar Afrika ta kudu ranar Juma’a, kuma na dawo jiya. Saboda lamarin Coronavirus din nan, dukkan kasashen duniya na daukar matakan kiyaye shigan cutar kasashensu.”

“A Afrika ta kudu, ba’a bari muka sauka daga cikin jirgi ba na tsawon mituna 30,”

“Jami’an kiwon lafiya sun shigo cikin jirgin kuma suka tantance kowa kafin aka amince muka shiga cikin kasar amma yayinda na dawo jiya a filin jirgin Nnamdi Azikwe, babu wanda ya tantancemu.”

“Kawai wata yar takarda aka bamu mu rubuta ko munada lafiya ko bamu da shi. Ta yaya zaku san ban da lafiya. Abin da ban toro.”

Sanatan ya ce gaskiya ya kamata a yi tsayin daka wajen hana cutar shigowa Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here