Babu Dan Sandan Da Ke Da Ikon Bincikar Wayoyinku – Hukumar ‘Yan Sanda

0
455

Daga Usman Nasidi.

TSOHUWAR mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jahar Legas, Dolapo Badmus ta bayyana cewa babu wani jami’in Dan sanda da ke da hurumin binciken wayar salular dan Najeriya, duk wanda ya yi haka ya ci zarafin yan kasa.

Dolapa ta bayyana haka ne yayin da take tattaunawa a taron murnar makon kafafen sadarwar zamani na shekarar 2020 da aka gudanar a jahar Legas a ranar Laraba, 26 ga watan Feburairu.

“Takurar da Yan sanda suke ma jama’an Legas suna bincikar wayoyinsu ya zama abin damuwa, bai dace ba kuma wuce gona da iri ne, yin hakan tamkar umartar mutum ya cire wandonsa ne don kawai kana bukatar yin aikin ka.” Inji ta.

A cewar Dolapo, hakan bai kamata ba musamman kasancewar wayar salula mallakin mutum ne, kuma sirrinsa ne, ta kara da cewa wayoyin salula na dauke da bayanan sirrin mutum kamarsu bayanan asusun banki da sauransu.

Sai dai Dolapo ta kawo inda ya zama wajibi yan sanda su duba wayar mutum, wannan kuma shi ne “Idan har akwai bukatar gudanar da bincike a kan hakan, sai dai kawai ka san a Najeriya mu ke, kuma har yanzu muna kokarin neman kwarewa a aikin Yan sanda ne.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here