Matawalle Ya Tursasa Shugabannin Makarantun Kwana Cin Irin Abincin Da Suke Ciyar Da Dalibai

0
478

Daga Usman Nasidi.

GWAMNA Bello Matawalle ya bukaci shugabannin makarantun sakandare da jami’an da ke ciyar da dalibai a jahar da su dinga ci daga cikin abincin da suke ciyar da daliban makarantun kwana ko kuma a sallame su

Hakan ya biyo bayan ziyarar ba-zata da Matawalle ya kai makarantun kwana na gwamnati a jahar, sannan ya ga irin abincin da ake ciyar da daliban

Ana dai ciyar da yaran ne da abinci mara inganci da tsafta

Gwamnan jahar Zamfara, Dakta Bello Mohammed Matawalle ya bukaci shugabannin makarantun sakandare da jami’an da ke ciyar da dalibai a jahar da su dunga ci daga cikin abincin da suke ciyar da daliban makarantun kwana ko kuma a sallame su.

Matawalle a yayin wani ziyarar bazata na kwanaki biyu da ya kai makarantun sakandare na kwana ta jahar, wadanda suka hada da Government Science Secondary School, Gusau da Government Girls School, Gusau ya nuna rashin jin dadi kan irin abincin da ake ciyar da dalibai cikin rashin tsafta da karancin inganci.

“Wajibi ne daga yanzu ku duna cin irin abincin da kuke ba daliban ku kuma zan sa a sanya muku idanu sosai saboda duk wanda ya saba ma wannan umurni na cin irin abincin dalibai za a sallame shi,” ya yi gargadi.

Matawalle ya ce abun haushi ne ganin cewa ana ciyar da daliban makarantun kwana abinci mara kyawu duk da makudan kudaden da gwamnati ke kashe wa a shirin ciyarwa.

Gwamnan ya yi gargadin cewa gwamnati ba za ta sake lamuntan irin wannan hali ba sannan cewa daga yanzu za ta yi maganin wadanda ta samu da hannu a aikin da baya bisa ka’ida na dafa abinci mara inganci ga daliban makaranta a jahar.

“Daga yanzu, shugabannin makarantun, jami’an ciyarwa da sauran jami’ai a fadin jahar sai sun dunga cin abinci iri guda da suka dafa ma daliban ko a kore su,” ya yi umurni.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here