Muhammad Sani Gazas Chinade, Daga Damaturu
RUNDUNAR ‘yan sandan jihar Yobe ofishinsu da ke garin Potiskum ta samu nasarar cafke wasu mutane uku da ake zargi da aikata fashi da makami da kuma garkuwa da mutane a yankin Karamar hukumar Fika ta yadda suka bukaci da a biya su zunzurutun kudi kimanin Naira Miliyan 2 matsayin kudin fansa don sako wani mutum mai suna Hodi Buba ko su hallaka shi.
Bayanin hakan dai na kunshe ne cikin wata takardar da ke dauke da sa hannun kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar ASP Dungus Abdulkarim da shigo hannun wakilinmu a Garin Damaturu.
Rundunar ‘yan sanda ta yi Karin haske da cewa, jami’ansu sun yi nasarar cafke wadanda ake zargin ne bayanin bayanai daga kwararrun jami’ansu masu binciken kwakwaf, yadda ya kai su ga cafke Musa Bello, Ya’u Bello da kuma Ahmadu Abdullahi wadda bayansu ma rundunar ta dukufa don gano sauran abokan aikata ta’assar da ta kai ha cafke su.
A wata mai kama da haka kuma a wani samame da ofishin ‘yan sandan Jihar dake ofishinsu na Shiyyar A dake tsakiyar garin Damaturu ta cafke wani mai suna Ahmed da aka fi sani da Kamisu Umar dake da zama a shago Tara da aka samu da laifin aikata fashi da makami ga wani mai suna Alhaji Yusuf a unguwar Ali Marami cikin garin Damaturu.Kamar yadda majiyar ‘yan sanda ta bayyana ta nuna kan cewar, Wanda aka kama din ya shiga gidan Alhaji Yusuf ne tare da tserewa kudadem da ba a San adadinsu ba tare da dauke wassu na’urori masu kwakwalwa Laptop guda biyu da Kuma wayoyin hannu guda 5 da sauran kayayyaki.
Bayanin ya kara da cewar, rundunar ‘yan sanda Na hobbasa don ganin ta cafke sauran abokansa don bincikarsu.Don haka ne rundunar ‘yan sandan ta kirayi jama’a da su ci gaba da bada goyon baya ga jami’ansu don ganin an dakike duk wani yunkuri Na masu aikata aika-aika dake cikin al’umma.