An Fara Tantance Masu Ziyarar Fadar Shugaban Kasa Don Gudun Coronavirus

0
421

Daga Usman Nasidi

FADAR shugaban kasar Najeriya ta fara gudanar da tantance ma’aikata da kuma bakin da ke ziyartar fadar da ke babban birnin tarayya Abuja biyo bayan samun bullar annobar cutar Coronavirus mai suna COVID-19 a Najeriya a ranar Juma’ar da ta gabata.

Rahotanni sun bayyana cewa an tura jami’an kiwon lafiya a kofar karshe ta shiga ofisoshin da ke cikin fadar shugaban kasa don su tabbatar ma’aikatan fadar gwamnatin tare da baki masu kai ziyara sun wanke hannayensu da ruwan wanke hannu na musamman domin kashe kwayoyin cututtuka da ke hannuwa.

Hakazalika jami’an kiwon lafiyan suna amfani da na’urar gwada zafin jikin mutum domin gwajin yanayin zafin ma’aikatan Villa da kuma baki, daga cikin wadanda aka yi ma wannan gwaji a ranar Talata akwai ministan kwadago, Chris Ngige wanda ya isa fadar da misalin karfe 4:50 na rana.

Majiyarmu ta bayyana cewa an samar da ruwan wankin hannun na musamman da na’urar gwajin yanayin zafin jikin dan adam a sakatariyar kungiyar gwamnonin Najeriya dake Abuja tun a ranar Juma’ar da aka fara samun bullar cutar a Najeriya.

Ma’aikatar kiwon lafiya ta kasa tare da cibiyar yaduwar cututtuka sun samar da cibiyar daukan matakan gaggawa domin magance yaduwar cutar a Najeriya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here