An Kama Mabaraciya Ngozi Makauniyar Karya

0
351
Musa muhammad Kutama, Daga Kalaba
‘YAN sanda a jihar Anambra sun kama wata mata mai suna Ngozi
Dike,shekara 37  da haihuwa tana yawo da yara suna yi mata jagora tana
bara ita makauniya ce domin ta rika samun kudi sadaka hannun jama’a.
Matar kamar yadda wakilinmu ya samu bayani daga bakin mai magana da yawun
rundunar ‘yan sandan jihar Anambra SP Haruna Muhammed ya sanar da batun wannan mata.
Ya ce an kama matar a kasuwar kauyen Oye Olisa da ke yankin Ogbunike
karamar hukumar , Oyi ta jihar. Ya ce”ranar Asabar 15 ga wannan wata an
kama wata mata mai suna Ndozi Dike na yawo da yara suna yi mata jagora
tana yawon bara matsayin ita makauniya ce alhali babu wata larurar
makanta a tare da ita”.inji shi
SP Muhammmamed ya baiyana sunayen yaran Blessing da Ezewanne mai shekara 8 da  ‘yar shekara 11

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here