Bakuwar Cutar Dabbobi Ta Bulla Jihar Jigawa

0
325
Rabo Haladu Daga Kaduna
WATA bakuwar cuta ta kashe shanu masu yawa a karamar hukumar Guri da ke jihar Jigawa.
Rahotanni na cewa daruruwan shanu ne suka mutu sakamakon cutar gwamnatin jihar ta musanta zargin.
Inda Muhammad Alhasan, kwamishinan ayyukan gona da raya karkara na jihar, ya bayyana wa manema labarai  cewa cutar ba wata bakuwa ba ce.
Ya ce akwai cututtukan da ake kira ‘Boru’ da ‘Sammore’ da ciwon hanta, kuma su ne wadanda aka sani a yankin Margadu inda aka samu rahoton mutuwar shanun.
Ya kuma ce a karamar hukumar Taura ma sun samu labarin mutuwar shanu biyar wadanda mutuwarsu ke da alaka da wadannan cutuka.
Kwamishinan ya musanta ikirarin da mutanen yankin suka yi na kai wa gwamnati kokensu game da cutar.
Yana cewa babu wanda ya kai rahoton cutar har sai da ta fara kashe dabbobinsu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here