Buhari Ya Rantsar Da Yemi Esan A Matsayin Sabuwar Shugabar Ma’aikatan Tarayya

0
340

Daga Usman Nasidi.

SHUGABAN kasa Muhammadu Buhari ya rantsar da Folashade Yemi Esan a matsayin sabuwar Shugaban ma’aikatan tarayya a ranar Laraba, 4 ga watan Maris.

An yi bikin rantsarwar Esan wacce ta karbi mulki daga hannun Winifred Ekanem Oyo Ita yan mintoci kadan kafin fara zaman majalisar zartarwa na mako.

An gudanar da taron ne a zauren majalisar zartarwa na fadar Shugaban kasa.

A baya mun ji cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari a da ren Juma’a ya amince da murabus din Misis Winifred Ekanem Oyo-Ita a matsayin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya daga ranar Alhamis 27 ga watan Fabrairun 2020.

Bayan haka, shugaban kasar ya kuma tabbatar da nadin Dakta Folashade Yemi-Esan wacce ta kasance shugaban ma’aikatan tarayyar na wucin gadi a matsayin tabbataciyar shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya (HoCSF).

Sakataren gwamnatin tarayya, Mista Boss Mustapha ne ya sanar da hakan a madadin sakataren dindin na na ofishin GSO, na ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Mista Olusegun Adekunle.

Hakan na zuwa ne watanni biyar bayan an dakatar da Oyo-Ita daga kujerarta a kan zargin aikata rashawa.

An dakatar da Oyo-Ita daga kujerar ta ne a ranar 18 ga watan Satumban 2019 bayan da aka mika wani rahoton zargin ta da hannu cikin bayar da wasu kwangila daga ofishinta ba bisa ka’ida ba.

A cewar sanarwa na amincewa da murabus din nata, Shugaba Buhari ya ce za a cigaba da binciken zargin da ake mata na hannu cikin aikata rashawar.

Shugaban kasar ya yi mata godiya bisa aikin da ta yi wa kasar ta kuma ya yi mata fatan alheri a ayyukan da za ta yi a gaba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here