-
Jabiru A Hassan, Daga Kano. An bayyana cewa hana barace-barace kan tituna barkatai da gwamnatin jihar kano ta sanar zai kawo tsafta wajen neman ilimin addini dana zamani musamman yadda gwamna Dokta Abdullahi Umar Ganduje yake daukar matakai na bunkasa ilimi a jihar tareda kyautata tarbiyya ta shirin bada ilimi kyauta kuma dole a jihar kano. Wannan bayani ya fito ne daga wasu malamai daga yankunan karkara da suka zantawa da Gaskiya Tafi Kwabo inda suka nunar da cewa ko shakka babu, gwamna Ganduje ya daura damarar tsaftace neman ilimin addinin musulunci da kuma kawo tsari mai gamsarwa ga yara ta yadda abin zai amfani al'uma ta kowane fanni. Malam Adamu Musa, malami mai koyar da karatun allo ga dalubai fiye da 50, yace mafiya yawan lokuta akan sami yara masu barace-barace cikin laifuka sannan wasun su ma basa yin karatu kuma tuni sun bar malaman su na ainihi da aka damka su garesu wanda hakan ko kadan ba daidai bane. Shi ma da yake nasa bayanin, malam Muhammadu Saye ya nunar da cewa hana barace-barace da gwamnatin kano tayi ba abin tada hankali bane, domin idan aka duba za'a fahinci cewa anyi hakan ne da kyakykyawar niyya wajen kawo tsafta a sha'anin neman ilimi da tarbiyya kamar yadda ake gani a kasashen musulmi na duniya. Wani almajiri da aka kai Kano daga jihar Katsina mai suna lawwali Abubakarya shaidawa wakilin mu cewa tun da aka kaishi kano bai yi karatu ba sai dai bara da neman kudi da zuwa gidajen mai wanda a cewarsa,hakan ta sanya yake ganin hana bara da gwamnatin jihar tayi abu ne da bai sabawa Shari'a ba. Sai dai wani bincike da Gaskiya Tafi Kwabo ta yi ya nunar da cewa mafiya yawan almajirai dake barace-barace ana kai su makarantar allo ne saboda iyayen su watau uwa da uba basu tare kuma babu wanda zai kula da ire-iren wadannan yara illa a Kai su makarantun allo batare da yin la'akari da inda ake kai su ba.