IGP Ya Fasa Kwan ‘Yan Bindigan Yankin Arewa Maso Yamma

1
645

Daga Usman Nasidi.

SUFETA Janar din ‘yan sandan Najeriya, Mohammed Adamu ya ce ‘yan bindigar da ke aika-aika a yankin Arewa maso Yamma din kasar nan duk mayakan Boko Haram ne da ISWAP.

A yayin magana a ranar Laraba yayin taro da manyan kwamandojin ‘yan sanda a kan harin kwanan nan da aka kai jihar Kaduna, Sufeta Janar ya ce sabbbin hare-haren da ake kawowa suna bukatar sabbin salon yaki don batar da ‘yan bindagar daga maboyarsu.

Shugaban ‘yan sandan ya kara da cewa, akwai tsananin amfani idan aka tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar nan.

Ya ce, “Na yanke shawarar zuwa Kaduna ne don tattaunawa da manyan jami’an da kuma sanin sabbin salon yaki da ta’addanci da suke shirayawa. Saboda mun san dai akwai alamun boko haram a ciki da kewayen jihar kuma hakan ne ya sa dole mu zage damtse don batar da su.”

“Shi ya sa a ranar 5 ga watan Fabrairun 2020 muka ziyarci da jin da ‘yan bindigar suke. A ranar 21 ga watan Fabrairun ne muka samu shiga sansanin ‘yan bindigar inda muka tarwatsa su da hadin gwiwar wata cibiyar tsaro. Wannan dabarar za mu ci gaba da amfani da ita wajen kawo karshen ta’addanci, in ji shi.

“Babu gudu kuma babu ja da baya. Abin da ya faru ba zai sake faruwa ba don ba za mu bari ba. Na samu labarin abin da ya kawo wannan harin ga kauyukan,”

Ya yi kira ga jama’a da su ba ‘yan sandan hadin kai wajen samar da gamsassun bayanai don shawo kan matsalar tsaro.

Ya kara da jawo hankulan ‘yan sandan da su dage wajen zuwa har sansanin ‘yan ta’addan don tarwatsa su.

Rahotanni sun bayyana cewa sifeta janar din ‘yan sandan Najeriya, ya samu ganawa da jami’an tsaro bayan harin ranar Lahadi da ’yan bindiga suka kai a wasu kauyukan jihar a ranar Lahadi. Harin ya yi sanadiyyar rasa rayukan mutane 51 a kauyukan kananan hukumomin Igabi da Giwa na jihar Kaduna din.

1 COMMENT

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here