Jihar Taraba Na Kan Gaba Wajen Ma’adinai – Yusuf Tanimu Njeke

0
640
Mustapha Imrana Abdullahi
AN bayyana jihar Taraba a matsayin jihar da ke kan gaba wajen zaman lafiya da kuma ma’adanan karkashin kasa.
Kwamishinan ciniki da masana’antu na jihar Taraba Honarabul Yusuf Tanimu Njeke ne ya bayyana hakan lokacin da yake ganawa da manema labarai a rumfar jihar Taraba a kasuwar duniyar kasa da kasa da ke Kaduna a Nijeriya.
Honarabul Yusuf Tanimu ya shaida wa manema Labaran cewa batun nan da ake yi cewa Gwamnan Taraba na yi na ku ba ni zaman lafiya in yi maku aiki, domin a samu ingantaccen ci gaban da kowa ke bukata.
Honarabul Yusuf Tanimu ya ci gaba da cewa shi da kansa ya zagaya kasuwar duniya ta kasa da kasa da ke ci a Kaduna inda ya ga abubuwa da dama daga kasashen duniya daban- daban.
“Na ga mutanen kasashen waje irin su Misra Egypt wato da sauran kassshe sun zo tare da kayayyakin gargajiyarsu da sauran kaya da yawa abin sha’awa kwarai”
Honarabul Tanimu ya bayyana zaman lafiyan da aka samu a Taraba da cewa ya samu ne sakamakon irin kwazon Gwamnan Taraba na yanzu inda yake aiki ba dare ba rana domin tabbatar da zaman lafiyan da ya haifar da ci gaban jjihar, arewaci da kasa baki daya.
“Muna kira ga daukacin al’ummar duniya da su zo jihar Taraba su zuba jari da fuskar masana’antu, ma’adinai, aikin noma, cinikayya, otal da yawon shakatawa da sauran fannonin rayuwa baki daya, kasancewar gwamnatin jihar Taraba a shirye take domin hada gwiwar da duk masu bukatar hakan”.
Ya kara da cewa a halin yanzu babu wata damuwa a jihar Taraba don haka kowa zai iya zuwa domin inganta al’amuran kasuwanci baki daya.
Kwamishinan ya kuma bayyana irin nasarorin da suka samu a shugabancin jihar inda ya ce a ma’aikatarsa sun samar da filin da dukkan mai son yin wata masana’anta zai iya zuwa domin gina masana’antar da yake bukata.
Ya kuma yi kira ga daukacin al’ummar jihar da su ci gaba da zaman lafiya da junansu ta yadda Gwamnan jihar zai samu zarafin aiwatar da aiki domin ci gaban jama’a.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here