Kungiyar Masu Rubuta Labarai Kan Hajji Da Umrah Za Ta Fara Buga Labarai Da Harshen Hausa A Yanar Gizo.

0
447
Jabiru A Hassan, Daga Kano.
KUNGIYAR masu rubuta labarai da rahotanni kan aikin Hajji da Umrah watau “Independent Hajjreporters” (IHR) ta shirya tsaf domin fara buga labari da suka shafi aikin Hajji da Umrah cikin harshen Hausa  a yanar gizo (Online), da kuma kafa tashoshin radiyo da talabijin domin kara bayyana abubuwan da ke faruwa wadanda suka shafi Hajji da Umrah a cikin gida da kuma kasa mai tsarki
A cikin wata muhimmiyar sanarwa da kodinetan kungiyar na kasa Malam Ibrahim Muhammad ya bayar, an bayyana cewa an yi tunanin fara wallafa labaran aikin Hajji da Umrah da harshen Hausa saboda a sami wani dandali na samun cikakku kuma sahihan labarai da rahotanni kan aikin Hajji da Umrah a nan gida Nijeriya da kuma kasa mai tsarki.
Haka kuma za’a kafa taashar radio da talabijin domin fadada aiyukan wannan kungiyar ta masu rubuta labarai kan aikin Hajji da Umrah musamman ganin yadda duniyar sadarwa take kara bunksa daidai zamani, sannan anyi hakan ne domin kawo labarai na Hajji da Umrah cikin sauri ta yadda maniyyata zasu fahimci aikin da kuma kokarin da hukumomin kula da aikin Hajji da kasa da na jihohi keyi domin su.
 Wakilinmu ya zanta da wasu maniyyata da ke shirin zuwa aikin Hajji bana dangane da wannan hangen nesa da kungiyar ta IHR ta yi, inda suka bayyana cewa anyi tunani mai kyau duba da yadda mafiya yawan alhazan Nijeriya sun fi jin harshen Hausa tare da yin fatan alheri ga wannan kungiyar ta masu rubuta rahitannin aikin Hajji da Umrah bisa kokarin da take yi wajen wallafa abubuwan dake faruwa ga maniyyata da masu yi masu hidima.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here