Likitoci A Jahar Kaduna Sun Shiga Yajin Aikin Dindindin

0
287

Usman Nasidi, Daga Kaduna.

KUNGIYAR kananan likitoci a jahar Kaduna, wato Association of Resident Doctors, ta fara yajin aikin sai baba ta ji daga ranar Laraba, 4 ga watan Maris sakamakon zargin gwamnatin jahar da suka yi da rashin cika alkawari.

Shugaban ARD, Emmanuel Joseph ya bayyana haka a garin Kaduna, inda ya ce sun dauki wannan mataki ne saboda gwamnati ta gaza cika alkawarin da ta dauka na gyara albashin likitocin, tare da magance wasu matsalolin kiwon lafiya a jahar.

“Don haka muka yanke hukuncin shiga yajin aikin dindindin, amma a irin halasci irin na mu, za mu cigaba da kula da marasa lafiya da suka kamu da cutar zazzabin Lassa, amma ba za mu sake karbar wani mara lafiya a asibiti ba, kuma zamu cigaba da sallamar wadanda aka kwantar saboda ba zamu iya kulawa da su ba.” Inji shi.

Tun a watan Oktoban 2017 ne gwamnatin jahar Kaduna tare da kungiyar ARD suka shiga wata yarjejeniyar warware dukkanin rikicin dake tsakaninsu, tare da iyakance iya lokacin da za’a dauka ana aiwatar da alkawurran domin cimma yarjejeniyar.

A cewar kungiyar, ta cika alkawarinta, amma gwmanati ta gaza a bangarenta, duk da cewa sun tuntubi gwamnatin jahar Kaduna a ranar 25 ga watan Nuwambar 2019, inda suka basu wa’adin watanni uku don su cika alkawarin, amma gwamnatin bata cika alkawarin ba.

“Sai da gwamnati ta tabbatar za mu shiga yajin aiki, shi ne ta kafa wata kwamiti a ranar 27 ga watan Feburairu, inda shugaban kwamitin ya rokemu mu daga musu kafa zuwa ranar 3 ga watan Maris an shekarar 2020 don ji daga gare su, amma har yanzu shiru.

“Don haka muka yanke hukuncin shiga yajin aiki tun da gwamnatin ta gagara cika alkawarinta.” Inji shi

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here