Masari Ya Zo Na Daya A Kasuwar Duniya Ta Kaduna

0
306
Mustapha Imrana Abdullahi
SAKAMAKON irin kwazon da gwamnatin Jihar Katsina ta nuna game da batun inganta harkokin ciniki da masana’antu a baki dayan Jihar da kasa baki daya yasa Gwamna Aminu Bello Masari a wannan shekarar ta 2020 ya halarci kasuwar duniya sa kansa inda ya yi wa duniya cikakken bayanin irin arzikin da Jihar ke da shi.
Gwamnan tare da jama’arsa sun halarci kasuwar duniya ta kasa da kasa da ke ci a kan titin Kaduna zuwa Zariya inda ya fayyace irin dimbin arzikin da yake dankare a cikin jihar.
Kamar yadda kowa ya sani jihar na da arzikin noma da kasuwanci tare da dimbin ma ‘adanai da duniyar sarrafa ma adinai me bukatar samu.
Sakamakon irin yadda jihar karkashin jagorancin Gwamna Masari ke bayyana kwazon aiki tare da bunkasa harkar noma ya sa nan take jagororin kasuwar suka bayyana jihar Katsina karkashin Aminu Bello Masari ta zamo ta daya. Abin da ke nuni da cewa masari ya zo kuma ya samu nasarar da ake bukatar a samu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here