Sun Yi Zanga-zangar Kyamatar Wanda Ya Zagi Annabi SAW

0
393
Rabo Haladu Daga Kaduna
WASU matasa a jihar Kano sun yi zanga-zangar neman a hukunta wani mawaki mai suna Yahaya Sharif-Aminu, wanda suka zarga da yi wa Annabi Muhammad S.A.W batanci.
Matasan sun yi cincirindo ne a gaban ofishin hukumar Hisbah, inda kwamandan hukumar ya tarbe su.
Tun a makon jiya ne wasu fusatattun matasa suka far wa gidan mahaifan mawakin a unguwar Sharifai da ke kwaryar birnin Kano tare da lalata abin da ke ciki.
Zuwa yanzu ba a san inda mawakin yake ba ko kuma halin da yake ciki.
Suna zargin mawak’in ne da rera wata waka, wadda aka yada a kafar sada zumunta ta whatsapp da ke aibata fiyayyen halitta, don haka suke cewa jininsa ya halatta.
Kwamandan hukumar ta Hisbah Shiekh Haruna Sani Ibn Sina ya bayyana cewa tuni suka kama mutum 10 game da lamarin tare da taimakon ‘yan sanda.
“Wakilan kwamishinan ‘yan sanda sun fada mana cewa sun kama mutum 10 wadanda ke da ruwa da tsaki a lamarin,” Ibn Sina ya shaida wa manema labarai.
Ya kara da cewa: “Shi ma wanda ya yi wakar (Yahaya Sharif-Aminu) ana kan matakin kamo shi.”
Zuwa yanzu rundunar ‘yan sandan Kano ba ta ce komai ba game da lamarin.
Daya daga cikin jagororin masu zanga-zangar Idris Yahya Ibrahim, ya bayyana cewa sun shaida wa kwamandan Hisbah bukatunsu kuma ya fada masu cewa za su yi duk mai yiwuwa wurin kama mawakin.
Kano jiha ce da ba ta daukar batun addini da wasa.  Duk da cewa an shafe tsawon lokaci ba a samu wani tunzurin addini ba, hukumomi na yin taka-tsantsan game da batun aikata sabo musamman saboda sanin tarihin Kano

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here