Za A Kara Bude Bankin Morgage A Zariya Da Kano – Dankane

0
526
Mustapha Imrana Abdullahi
WANI daga cikin shugabannin Bankin gina gidaje na tarayyar Nijeriya Alhaji Umar Dankane Abdullahi, ya bayyana aniyar da suke da ita na bude karin ofishin Bankin a garuruwan Kano da Zariya cikin Jihar Kaduna domin jama’a su ci gaba da cin gajiyar ayyukan Bankin.
Alhaji Umar Dankane ya bayyana hakan ne a garin kaduna lokacin da ya halarci bikin ranar Bankin a kasuwar duniya ta kasa da kasa da ke Kaduna.
Alhaji Dankane wanda ya wakilci shugaban Bankin Alhaji Ahmed Musa Dangiwa ya ce sun yanke shawarar kara wadannan Ofisoshi biyu ne saboda irin bukatar da ake da ita domin ma’aikata da sauran Jama’a su ci gaba da cin gajiyar tsare tsaren Bankin cikin sauki.
Ya kara da cewa suna ba ma’aikata bashin gyaran gidaje da kuma sama masu da gidaje a gine kuma har da kungiyoyin Gama kai ma suna cin gajiyar Bankin domin akwai shirin da aka yi wa kowa kasancewar ana bukatar kowane dan kasa ya rika yin ajiya a Bankin indai yana samun kudin da duka kai naira dubu uku duk tanajen tanajen na nan a tsare domin Jama’a.
Sai dai ya yi kira ga Gwamnatin tarayya da ta kara yawan harin Bankin kasancewar jama’ar Nijeriya sun yi yawa a halin yanzu kuma akwai bukatar samun gidaje da yawa a yanzu.
Da yake tofa albarkacin bakinsa shugaban kungiyar manyan ma’aikata (TUC)na Jihar Kaduna Kwamared Shehu Muhammad cewa ya yi hakika ma’aikata a Jihar kaduna sun ci gajiyar wannan Banki domin wasu tuni aka ba su kudin gyaran gidajensu a wannan Banki.
(Don haka ya dace Gwamnati ta zuba manyan kudi a Bankin domin kara fadada cin gajiyarsa).

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here