An Damke Kwarto Mai Shigar Mata

0
780
WATA babbar kotun gwamnatin tarayya da ke a Unguwar Nasarawa birnin Kebbi, Jihar Kebbi, ta mika wani mutum mai shekaru 24 mai suna Abubakar Garba, saboda aikata wani laifi da ya yi na shigar mata sanye da hijabi ya shiga gidan makwabcinsa da nufin ya yi wa matar makwabcin nasa fyade.
Lamarin dai ya faru ne a unguwar Asarara, cikin karamar hukumar Birnin Kebbi.
Jami’an ‘yan sanda ne suka kama mutumin bayan da aka kai masu korafin faruwar lamarin, wanda mai gidan Aliyu Hakimi ya kai koke da abin ya faru cewa yana zargin Abubakar Garba da shiga cikin gidansa inda ya yi shigar mata da nufin ya yi lalata da matarsa.
Amma sai matar mai suna Hauwa Aliyu, ta ki amincewa da shi kuma nan take ta nemi taimako daga makwabta abin da ya yi sanadiyyar kama Abubakar Garba.
A cikin bayaninsa Abubakar Garba ya amince da aikata laifin amma ya roki kotu da ta saukaka masa a game da laifin.
 Babban Alkalin kotun Mu’awaya Shehu Birnin Kebbi ya mika wa ‘yan sanda mai laifin a wurinsu zuwa sati mai zuwa lokacin da za a yanke hukuncin karshe.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here