Isah Ahmed Daga Jos
AKALLA ma’aikata masu aikin rushe gini tare da kariyar jami’an tsaro daga jami’ar Jos, sun rushe gidaje sama da 50 a garin Narkuta da ke Karamar Hukumar Jos ta Arewa a Jihar Filato, a ranar asabar din da ta gabata.
Idan ba a manta ba, makonni biyu da suka mun buga labarin rikicin da ya faru a garin na Narguta, wanda ya yi sanadin rasa ran mutum daya, kan takaddamar mallakar fili da ake yi, tsakanin jami’ar Jos da al’ummar garin Narguta.
Da yake zantawa da ‘yan jarida kan wannan al’amari, a fadarsa da ke garin na Narkuta Sarkin na Narguta Injiniya Muhammad Bello ya bayyana takaicinsa kan faruwar wannan al’amari.
Ya ce a safiyar ranar asabar da safe sai suka tashi suka ga jami’an tsaro, sun kewayemu tare da ma’aikata daga jami’ar Jos da motocin rushe gini, suka fitar da mutanensu daga gidajensu suka kama rushe gidajen.
Ya ce a wannan abu da aka yi mana wanda aka take mana haqqinmu na dan adam, an rusa mana gidaje a kalla sama da guda 50.
‘’ A matsayinmu na masu son zaman lafiya da bin doka da oda muna bin dukkan hanyoyin da suka kamata, wajen ganin an warware wannan takaddama kan mallakar wannan fili. Don haka muna kira ga masu ruwa da tsaki kan wannan al’amari, na ciki da wajen Jihar Filato su dubi wannan abu da aka yi mana, na rushe mana gidaje wanda ya jefa iyalanmu cikin mawuyacin hali, don warware wannan takaddama’’.
A lokacin da aka tuntubi jami’in hulda da jama’a na Jami’ar ta Jos, Mista Abdllahi Abdullahi don jin ta bakinsa kan wannan al’amari, ya bayyana cewa ba zai iya cewa komai ba, domin yanzu yana hutu ne.
Jami’ar ta Jos da al’ummar garin na Narkuta dukkansu kowa yana ikirarin cewa shi ne ya mallaki wannan fili da ake takaddama, wanda al’ummar garin na Narkuta suka yi gine gine a ciki.
A wata sanarwa da al’ummar na garin na Narakuta suka fitar, sun bayyana cewa sun sayi wannan fili ne, daga kamfanin Ron Properties Nig LTD a madadin Iyalan Wakili Jatau da suka bashi hakkin sayar da filin, da sune asalin suke da mallakarsa.
A yayinda itama a wata sanarwar da ta fitar da ke dauke da sanya hanun mataimakin babban magatakardar Jami’ar ta Jos, Wilson Yale ta bayyana cewa Jami’ar ta Jos ta sayi wannan fili ne daga kamfanin yin jan bulo na Nigeria Bricks and Clay Product LTD ta hanun kamfanin sayar da kadarorin gwamnati na BPE