Ba Ni Da Hannu A Cire Sarki Sanusi – Buhari

0
498
Rabo Haladu Daga Kaduna
SHUGABAN kasa Muhammadu Buhari ya bayyana cewa ba shi da hannu a tsige tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II.
Mai magana da yawun shugaban kasar Malam Garba Shehu ne ya wallafa haka a shafinsa na Twitter a ranar Laraba, inda ya bayyana cewa duka maganganun da ake yadawa ba gaskiya ba ne kuma siyasa ce.
Ya bayyana cewa shugaban kasa bai taba katsalandan a cikin harkokin wata jiha a kasarnan ba sai dai idan hakan ya shafi tsaron kasa baki daya.
Garba Shehu ya bayyana cewa,  nada sarki da kuma tsige shi ya rataya ne kan gwamnatin jihohi ba na tarayyaba.
Ya kuma bayyana cewa ba adalci bane masu hamayya da gwamnati su rinka kokarin alakanta abin da ya faru a jihar Kano da kuma gwamnatin tarayya.
Shugaban kasar kuma ya yabi mutanen Kano da dattakun da suka nuna nakin tayar da zauna tsaye bayan tsige sarki sanusi.
Ana dai ganin cewa wannan sakon da Garba Shehu ya wallafa bai rasa nasaba da kalaman tsohon gwamnan jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso wanda ya zargi shugaban kasar da bayar da umarnin cire Muhammadu Sanusi na II.
Ya kara da cewa a matsayinsa na tsohon soja kuma shugaban kasa a mulkin soja, Shugaba Buhari ya fahimci cewa a tsarin dimokradiyya, gwamnati ce a tsakiya kuma bai kamata ta yi katsalandan ba a harkokin gwamnatocin jihohin kasa 36.
Dukkansu suna da iko da kundin tsarin mulkin kasa ya ba su.
A cewar mai magana da yawun shugaban, Buhari ya yi addu’ar samun ci gaba ga masarautar da gwamnatin jihar da ma al’ummarta.
A ranar Litinin ne, gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya sauke Sarki Sanusi II tare da maye gurbinsa da Aminu Ado Bayero – dan marigayi Ado Bayero.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here